Mazauna ‘Yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, sun cigaba da
zama a gidajen su ranar litinin da ta gabata, kamar yadda masu
fafutukar kafa kasar Biafra suka bada umurni, duk kuwa da
ikrarin shugabannin yankin cewa an kawo karshen matsalar.
Bayanai daga wasu garuruwan yankin sun ce, ko a ranar litinin
da ta gabata mutane sun kaurace wa shagunan su da wuraren
sana’ar su domin kauce wa harin ‘yan kungiyar IPOB.
A karshen makon da ya gabata ne, Majalisar Sarakunan
Gargajiya ta Jihar Anambra ta sanar da cewa, haramcaciyar
kungiyar IPOB ta dage haramcin gudanar da harkoki a ranakun
litinin da ta sa a yankin.
Shugaban majalisar Nnaemeka Achebe, ya ce IPOB ta dauki
matakin ne bayan ganawar da ta yi da wakilan su da na limaman
addini, wadanda su ka yi alkawarin samo maslaha dangane da
matsalar tsaron da ta addabi yankin da kuma tilasta wa jama’a
zaman gida.
Basarake Achebe, ya ce bayan ganawa da wakilan kungiyr
IPOB, nan take su ka kira ‘yan kungiyar su ka bukaci su ajiye
makaman su domin rungumar tattaunawa.