Home Labarai ‘Yan Ta’Adda Sun Sace Mutane Da Ke Bude-Baki a Masallaci

‘Yan Ta’Adda Sun Sace Mutane Da Ke Bude-Baki a Masallaci

61
0

‘Yan ta’adda sun kai hari wani masallaci da ke kauyen Baba Juli
a karamar Hukumar Bali ta jihar Taraba, yayin da masallata ke
bude baki a daren Talatar da ta gabata, inda su ka kashen mutane 3 sannan su ka yi awon gaba da wasu.

Wata majiya ta ce, mahara kimanin 50 ne su ka afka cikin
masallacin, inda su ka yi awon gaba da masallata da dama zuwa
wani wuri da ba a sani ba.

Rahotanni sun ce ko a watan da ya gabata, ‘yan ta’addan sun kai
hari a garin Baba Juli, amma aka tilasta masu ficewa bayan
musayar wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Taraba DSP Usman
Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ya na
jiran karin bayani daga helkwatar ‘yan sanda ta karamar
hukumar Bali.