Home Labaru Sanata Ahmed Lawan Ya Taya Musulmai Murnar Sallah

Sanata Ahmed Lawan Ya Taya Musulmai Murnar Sallah

512
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar bikin babbar sallah.

A cikin sakon sa na taya murna da ya fito daga bakin mai magana da yawun sa Ola Awoniyi, Sanata Lawal ya gargadi musulmi cewa kada su shagala su manta da mahimmancin bikin babbar Sallah.

Sanatan, ya nemi daukacin musulmin Nijeriya su yi koyi da  rayuwar Annabi Ibrahim, wan da ya kasance mafarin gudanar da bikin babbar Sallar Layya.

Ya kuma gargadi al’ummar Nijeriya su tsaya tsayin daka wajen sanya tsananin kishi tare da tabbatar da ci-gaban kasa baki daya, su kuma so junan su wajen tabbatar da hadin kai, yayin da Nijeriya ke warware matsalolin da su ka yi mata dabaibayi.