Home Labaru Diezani Ta Ce Ba Ta Saci Ko Sisin Kobon Nijeriya Ba

Diezani Ta Ce Ba Ta Saci Ko Sisin Kobon Nijeriya Ba

360
0
Diezani Alison Madueke, Tsohuwar minister Man Fetur
Diezani Alison Madueke, Tsohuwar minister Man Fetur

Tsohuwar minister man fetur Diezani Alison Madueke, ta karyata zargin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da hukumar EFCC su ka yi mata cewa ta yi sama da fadi da dukiyar talakawan Nijeriya a lokacin da ta ke aiki.

Diezani ta bayyana haka ne, yayin da ta zanta da fitaccen dan jarida Dele Momodu, inda ta karyata zargin da ake yi mata na sace dukiyar talakawa.

Tsohuwar Ministar ta karyata zargin cewa ta yi almubazzaranci da dukiyar man fetur, ta na mai cewa ita matar aure ce kuma bata da dabi’ar fataken dare.

Diezani, ta kuma karyata zargin yin sama da fadi da dala biliyan 20 na kudin man fetur, ta na mai bugun kirji da cewa duk wanda ya ke da hujja a kan ta saci kudi ya fito ya bayyana wa duniya.

A karshe ta nuna rashin jin dadi game da yadda wasu ‘yan Nijeriya ke zagin ta, duk kuwa da irin kokarin da ta yi na azurta da yawa daga cikin su.

Leave a Reply