Home Labaru A Guji Tsattsauran Ra’ayi Na Tashin Hankali – Buhari

A Guji Tsattsauran Ra’ayi Na Tashin Hankali – Buhari

293
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Yayin da mabiya addinin Islama ke ci-gaba da gudanar da bikin babbar Sallah, shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa a guji tsauttsauran ra’ayi na tashin hankali.

A cikin sakon sa na goron sallah ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya, shugaba Buhari ya ce tsauttsauran ra’ayi mai cike da tashin hankali na daya daga cikin miyagun matsalolin da addinin Islama ke fuskanta a yanzu.

Buhari ya yi hani tare da gargadin mabiya addinin Islama su nesanta kawunan su wajen sauraron koyarwar masu tsauttsauran ra’ayi na tada tarzoma, ko kuma mummunar husuma a tsakanin al’umma.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma tunatar da al’ummar musulmi cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali tambari ne na addinin musulunci da ya wajaba duk mabiyan sa su kare martabar sa ta hanyar kaurace wa tsatstsauran ra’ayi mai cike da tarzoma, domin kuwa sabanin hakan batanci ne ga addinin.

Haka kuma, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan da wasu gwamnonin Nijeriya, sun bukaci daukacin al’ummar musulmi su cigaba da addu’o’in neman kawo karshen ta’addanci da ya yiwa Nijeriya dabibayi.