Ƙyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard ya koma yin atisaye a lokacin da Gunners ke shirin karawa da Inter Milan a Champions League ranar Laraba.
Ɗan wasan ya fara jinya a cikin watan Satumba, bayan da ya ji rauni lokacin da yake buga wa kasarsa tamaula, inda rashin ƙyaftin ɗin ya taɓa ƙwazon Gunners a wasanninta.
Arsenal ta samu maki ɗaya daga tara da yake kasa a karawa uku a Premier League, wadda ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da Newcastle da canjaras da Liverpool.
Kafin Odegaard ya ji rauni, Arsenal ta yi wasa huɗu da yin nasara uku da canjaras ɗaya, sai dai bayan da yake jinya, Gunners ta buga karawa 12 da nasara bakwai da canajaras uku aka doke ta wasa biyu.
Hakan ya sa Arsenal ta yi kasa zuwa mataki na biyar a teburin Premier League a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
Idan Gunners ta buga Champions League da Inter Milan ranar Laraba, daga nan za ta je Stamford Bridge ta kara da Chelsea a Premier League ranar Lahadi.
Sai kuma Arsenal ta karɓi bakuncin Nottingham Forest a dai Premier League ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba.