Home Labaru Matakin Kariya: El-Rufai Ya Umarci Ma’aikatan Jihar Kaduna Su Yi Aiki Daga...

Matakin Kariya: El-Rufai Ya Umarci Ma’aikatan Jihar Kaduna Su Yi Aiki Daga Gida

146
0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci ma’aikata ‘yan ƙasa da mataki na 14 su fara aiki daga gida daga yau Litinin sakamakon ɓarkewar annobar korona a zagaye na biyu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Muyiwa Adekeye, ya sanya wa hannu ta ce an ɗauki matakin ne bayan Gwamna Nasir El-Rufai, ya amince da sabuwar dokar kulle a jihar.

Da ma tuni gwamnatin ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu a jihar, kuma sanarwar ta ce za su ci gaba da kasancewa a garƙame har sai abinda hali ya yi.

Daga cikin tanadin sabuwar dokar, wuraren motsa jiki da wuraren taron biki da na shaƙatawa za su kulle har sai baba ta gani, kazalika wuraren cin abinci ma za su riƙa sayarwa ne a mazubi domin ci a gida, ba za a ci a wurin ba, haka nan su ma otel-otel za su buɗe amma za su rufe wuraren cin abincin su, sai dai ɗakunan kwana kawai.

Sauran abin da dokar ta ƙunsa sune Wajibi ne wuraren addini su samar da kayan wanke hannu da bayar da tazara, sannan kuma a rage yawan masu shiga sallar jam’i ko addu’ar coci kar su wuce awa ɗaya, kana sa takunkumi wajibi ne idan za a fita daga gida.

Taron jama’a haramun ne, kuma dole ne wuraren kasuwanci su tanadi man wanke hannu da kuma na’urar duba zafin jikin mutum.