Home Labaru Samun Gurbin Karatu: Shugaban Neco Ya Ce Bai Kamata Turanci Da Lissafi...

Samun Gurbin Karatu: Shugaban Neco Ya Ce Bai Kamata Turanci Da Lissafi Su Zama Dole Ba

23
0
NECO

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi ya yi kira da a daina amfani da tsarin tilasta samun sakamako a darussan Turanci da Lissafi kafin samun gurbin karatu a manyan makarantun Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron Kungiyar Makarantun Islamiyyah a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar.

Ya kuma yi kira da a kafa kotu ta musamman don hukunta masu magudin jarrabawa domin a cire tarnakin da ake fuskanta wajen gurfanarwa da kuma hukunta masu aikata laifin satar jarabawar.

Farfesa Wushishi, a cikin makalar da ya gabatar mai taken: “Yadda za a magance magudin jarrabawa domin ci gaban kasa”, ya ce, “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta rage yawan tasirin da take ba takardu a kan komai a kasar nan, wajen tantancewa da kuma ba da sakamako ga dalibai da ma’aikata.

Shugaban na NECO ya lura cewa tsare-tsare da manufofin gwamnati a kan harkar ilimi na bukatar garanbawul, inda ya ce akwai bukatar samar da isassun kayan aiki a makarantun gwamnati don inganta harkar koyo da koyarwa.