Home Labaru Gasar Firimiya: Aubameyang Ya Karya Kwari

Gasar Firimiya: Aubameyang Ya Karya Kwari

11
0
PREMIER

Arsenal ta yi nasarar doke Norwich City 1-0 a wasan Premier League karawar mako na hudu ranar Asabar, kuma karon farko da ta yi nasara a fafatawar bana.

Hakan zai rage matsi ga koci Arteta da kungiyar wadda aka doke ta wasa ukun da ya sa ta koma ta karshen teburi kafin fafatawar ranar Asabar a Emirates.

Gunners ta ci kwallon ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang da hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata.

Arsenal ta yi rahin nasara da ci 2-0 a gidan Brentford a wasan farko da fara Premier ta bana, sannan Chelsea ta doke Gunners 2-0 a karawar mako na biyu a Emirates.

Haka kuma Gunners ta kwaso kwallo 5-0 a Manchester City a Etihad, kenan ta buga wasa uku a karon farko ba ta yi nasara ba tun bayan 1954, kakar da ta fara mai muni.