Home Labaru Samar Da Rugage: Walid Jibril Ya Ce Shi Ne Mafita

Samar Da Rugage: Walid Jibril Ya Ce Shi Ne Mafita

186
0

Shugaban kwamitin amintattu na Jam’iyyar  PDP Sanata Walid Jibrin, ya ce saboda yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali ne yake  goyon bayan shirin kafa rurage ga makiyaya na gwamnatin tarayya.

Ya ce matakin da ya dauka na amincewa da shirin  samar da ruga, ya janyo cece-kuce, a sassa daban daban na Najeriya, musamman kasancewar sa amintacce ga jam’iyyar sa ta  PDP.

Ya kara da cewar batun kafa ruge ga makiyaya ba batun jam’iyyar PDP ko APC ba ne, ya kara da cewa shugabannin Fulani ba za su iyi  barin alummar  su fada cikin ayyukan garkuwa da mutane da sauran ayaukan ta’addanci a Najeriya ba.

Walid Jibrin,  ya ce a matsayin san a dan kabilar Fulani ya zama wajibi ya marawa duk wani shiri na gwamnatin tarayya baya,  musamman akan yadda za a taimakawa fulani makiyaya .

Ya ce ya lura kalaman sa na goyon bayan kafa rugage ga makiyaya ya janyo cece-kucen da bai da wani amfani.

Ya tabbatar da cewar a matsayin sa na daya daga cikin shugabannnin kabilar Fulani duk wani abu da zai da dada masu rai, ya zama wajibi ya  mara masa baya.
e