Home Labaru Damfara: EFCC Ta Kama Oyediran Da Kasar Amurka Ke Nema Ruwa A...

Damfara: EFCC Ta Kama Oyediran Da Kasar Amurka Ke Nema Ruwa A Jallo

240
0
Hukumar EFCC Ta Kama Oyediran Da Kasar Amurka Ke Nema Ruwa A Jallo
Hukumar EFCC Ta Kama Oyediran Da Kasar Amurka Ke Nema Ruwa A Jallo

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama wani shahararren dan damfara Oyediran da hukumar binciken sirri na kasar Amurka ke nema ruwa a jallo.

Karanta wannan: Yaki Da Rashawa: EFCC Za Ta Daukaka Kara A Kan Waripamo Owei-Dudafa Da Kotu Ta Saki

Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce kwamandan hukumar na shiyya Isyaku Sharu ya sanar da haka a lokacin da yake bada rahoto kan aikin da hukumar da hadin gwiwar FBI na kasar Amurka ke yi na yaki da damfarar yanar gizo.

Wannan na daga cikin damarar da hukumar EFCC ta dauka na yaki da ‘yan damfara musamman ta yanar gizo.

Ya ce makwanni 3 da suka gabata hukumar FBI ta rubuto mata takardar neman hadin gwiwa wajen kama wasu ‘yan Nigeria da suka shahara wajen damfara.

Ya kara da cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa Oyediran ya amfana da akalla naira milliyan 60 na damfara ta hanyar hada-hadar kudade.