Home Labaru Samamen Lagos: An Kama Wani Fasto Da Ya Daure Mutane Da Sarka...

Samamen Lagos: An Kama Wani Fasto Da Ya Daure Mutane Da Sarka A Cocin Sa

623
0
Samamen Lagos: An Kama Wani Fasto Da Ya Daure Mutane Da Sarka A Cocin Sa
Samamen Lagos: An Kama Wani Fasto Da Ya Daure Mutane Da Sarka A Cocin Sa

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta kama wani fasto bisa zargin sa da hannu wajen daure wasu mutane da sarka a wani coci da aka maida sansanin azabtar da jama’a jihar Lagos.

Yayin samamen da su ka kai harabar cocin, jami’an ‘yan sanda sun ceto mutane 15 da su ka samu daure a cikin mari.

Wasu bayanai na cewa, akwai wadanda su ka shafe tsawon shekaru biyar su na shan azaba a sansanin.

Jami’an ‘yan sanda dai sun kai samamen ne, biyo bayan wasu bayanan sirri da su ka samu cewa wani fasto ya na gana am wasu mutane azaba a wani sansani. Tuni dai Samamen ya kai ga kama faston mai suna Sunday Joseph, yayin da aka kama wasu mutane 10 da ke aiki a cocin, a matsayin masu taimaka wa faston wajen gana wa mutanen azaba.