Home Labaru Ba Za Mu Fasa Shirin Binciken Matafiya Su Nuna Katin Shaida Ba...

Ba Za Mu Fasa Shirin Binciken Matafiya Su Nuna Katin Shaida Ba – Buratai

487
0
Ba Za Mu Fasa Shirin Binciken Matafiya Su Nuna Katin Shaida Ba - Buratai

Babban Hafsan Hafsoshin Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya ce duk da korafe-korafen da jama’a ke yi, sojoji ba za su dakatar da shirin su na fara binciken matafiya ba.

Sojojin Nijeriya dai za su fara tare manyan hanyoyin Nijeriya, da nufin neman ganin katin shaidar matafiya da ke cikin motocin zirga-zirga.

Buratai ya sha alwashin ne, a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Majalisar wakilai a karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Tsaro na majalisar Abdulrazak Namdaz.

Ya ce sun fito da shirin ne, domin kokarin zakulo ‘yan Boko Haram da su ka tsere da kuma gano wasu tantiran masu aikata laifuffuka daban-daban a Nijeirya.

Babban Jami’in Soji U.S Mohammed da ya wakilci Buratai a Majalisar, ya ce ba wai sojoji za su kafa shingaye ne a kan hanya su hana motoci wucewa ko haddasa cunkoso kamar yadda ake tunani ba.