Home Labaru Jam’iyyar APC Ta Fara Zawarcin Atiku Abubakar

Jam’iyyar APC Ta Fara Zawarcin Atiku Abubakar

769
0
Jam’iyyar APC Ta Fara Zawarcin Atiku Abubakar
Jam’iyyar APC Ta Fara Zawarcin Atiku Abubakar

Masana fannin shari’a da sauran al’ummar jihar Adamawa na ci-gaba da maida martani a kan hukuncin da kotun koli ta yanke game da shari’a Atiku Abubakar da shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP dai ta ce ta yi mamakin hukuncin da alkalan su ka yanke a cikin kankanin lokaci, kamar yadda sakataren jam’iyyar na jihar Adamawa Abdullahi Adamu Prembe ya bayyana.

To sai dai kuma, ga ‘yan jam’iyar adawa ta APC a nasu bangaren, suna ganin hukuncin ya yi daidai.

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC Ahmad Lawal, ya ce yanzu za su shiga zawarcin Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar APC tunda shari’a ta kare.

To ko ya masana shari’ar kuma ke kallon yadda aka yanke wannan hukuncin? Barr Sunday Joshua Wigra lauya mai zaman kansa, ya ce ko ba komai akwai darasin dauka a wannan hukunci.

Leave a Reply