
A ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta na shekara ta 2019 ne za a yi bikin Babbar Sallah a Nijeriya, kamar yadda Sakataren Kwamitin Ganin Wata na Nijeriya Malam Yahaya Boyi ya shaida wa manema labarai.
Sai dai bai yi karin haske game da tabbacin ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a Nijeriya ba, ko kuma ya dogara ne da ganin watan Saudiyya.
Ko da ya ke kwamitin ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa, ranar Juma’a ce 1 ga watan Dhul Hijjah, 1440 BH.
Haka kuma, kwamitin ya wallafa wani sako da ke cewa ba a samu labarin ganin jinjirin watan a fadin Nijeriya ba a ranar Alhamis da ta gabata.
Ya
ce bayan tuntubar malamai, an ayyana ranar 2 ga watan Agusta na shekara ta 2019
a matsayin 1 ga watan Dhul Hiijjah, bisa dogaro da ganin watan Saudiyya.
You must log in to post a comment.