Home Labaru Sallamar Ministoci: Lai Muhammad Ya Ce Buhari Bai Da Wani Shiri Na...

Sallamar Ministoci: Lai Muhammad Ya Ce Buhari Bai Da Wani Shiri Na Sauke Ministocin Sa

259
0
Lai Mohammed, Ministan Labarai Da Al’adu

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya ce babu wani shiri da shugaba kasa Muhammadu Buhari ke yi na sallamar ministocin sa daga aiki.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya umarci dukkan ministocin sa su aika da cikakkun bayani a kan ayyukan da suka gudanar na tsawon shekaru 4.

Shugaban kasa Buhari ya umarci ministocin sa ne su aika da takardun zuwa ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Wannan sanarwa, ita ta sa aka rika hasashen cewa, babu mamaki shugaban kasa Buhari zai sauke ministocin sa ne daga aiki, kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai kuma a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, Lai Muhammad ya shaida wa manema labarai na fadar shugaban Kasa cewa, Ministoci na nan daram babu wani shirin tsige su ko sauke su daga aiki.