Home Labaru Kisan Kai: Jami’an Kastelea Sun Kashe Wani Dan Acaba A Zariya

Kisan Kai: Jami’an Kastelea Sun Kashe Wani Dan Acaba A Zariya

289
0

Wasu jami’an hukumar kula da cunkuson ababen hawa da samar da dokar tsaftace na jihar Kaduna KASTELEA sun kashe wani dan Acaba tare da raunata wasu mutum biyu a Zaria.

Wani bincike da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya gudanar ya nuna cewa, jami’an KASTELEA da aka aje domin gudanr da aiki a Tudun Wadan zariya ne suka haddasa faruwar kashe dan acaban tare da raunata mutanan biyu.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa manema labarai cewa, jami’an KASTELEA sun biyo wani dan acaba daga Tudun Wada suka kuma cimma sa a kwanar Alhudahuda da ke garin Zariya, sannan wani mai Keke Napep ya zo ya doki motar jami’an na KASTELE, lamarin da ya saka direban da wata fasinja suka samu raunuka.

Sai dai, an garzaya da wadanda suka samu raunin zuwa asibitin koyar wa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Tudun Wada Zaria domin a duba lafiyar su.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa, mutuwar dan acaban ta harzuka abokan sana’ar sa, wadanda hakan ya sa suka yi dandazon zuwa fadar sarkin zazzau Dakta Shehu Idris domin kai koken su.

Da yake jawabi ga dandazon ‘yan acabar shugaban karamar hukumar Zariya Aliyu Idris,ya bukaci matasan su kwantar da hankalin su tare da yi masu alkawarin cewa, za a gudanar da bincike a kan abinda ya faru a kuma dauki mataki a kai.