Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, yace gwamnatin tarayya a baya-bayan nan ta kuɓutar da mutane sama da dubu 1 daga hannun ‘yan ta’adda ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi Malamai da Dalibai 22 na jami’ar Gusau da ke jihar Zamfara, da aka kubutar da su daga hannun ‘yan bindiga a ranar Lahadi.
Idan ba’a manta ba tun a ranar 22 ga watan Satumbar 2023 ne ‘Yan bindiga suka shiga jami’ar tare da yin awon gaba da sama Dalibai da Malamai 30.
A nasa jawabin shima da ya kasance a Jami’ar yayin karbar Dalibai da Malaman, mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mani Mummuni, ya jajantawa iyalai da kuma hukumar makarantar bisa abinda ya faru.
Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kubutar da sauran Daliban da aka sace a wasu makarantun a Najeriya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Yazid Abubakar ya fitar, ya bada tabbacin cewa rundunar zata ci gaba da iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da sauran daliban da ke hannun masu garkuwa da mutanen.