Home Labaru Matsalar Tsaro: Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki

Matsalar Tsaro: Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki

314
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudurin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro dake da alaka da siyasa kabilanci da kuma ta’addanci.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar dake fafutukar nuna goyon bayansa da mataimakinsa Osinbajo a fadarsa dake Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar dake fafutukar nuna goyon bayansa da mataimakinsa Osinbajo

Sannan ya bukaci dukkanin ‘yan Najeriya da su marawa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin ta magance matsaloli da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Ya ce ba bambancin yare addini ko kabila ne abin da ya fi muhimmanci ba, samar da yanayi mai kyau da zaman lafiya shi zai kawo ci gaban kasa, da kwanciyar hankali.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na ci gaba da aiki ba dare ba rana dan ganin ta cika dukkanin alkawuran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe. 

A nasa bangaren shugaban tawagar da ta kai ziyarar, Usman Ibrahim, ya bukaci shugaba Buhari ya tuna da ‘ya’yan kungiyar a mataki na gaba da ya dauka a mulkinsa.