Home Labaru Ilimi Sakamakon Talauci: Wani Matashi Ya Hallaka Kan Sa A Jihar Kebbi

Sakamakon Talauci: Wani Matashi Ya Hallaka Kan Sa A Jihar Kebbi

3046
0

Wani matashin dalibi dan shekaru 29 a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Waziri Umaru da ke Birnin kebbi mai suna Solomon Benedict, ya halaka kan sa sakamakon fuskantar matsanancin talauci.

Benedict dai ya hallaka kan sa ne ta hanyar shan maganin kwari a cikin madara, inda abokan shi sun yi kokarin ceto rayuwar shi amma abin ya ci tura.

Yayin da ya ke zantawa da manema labarai, wani abokin marigayin ya bayyana cewa, sun lura da cewa mamacin ba ya da sauran sukuni, sai daga baya su ka lura cewa ya gauraya maganin kwari a cikin abin shan sa.

Bayanai sun nuna cewa, matashin ya rasa ran sa ne a lokacin da ake kokarin kai shi asibiti mafi kusa domin ceto rayuwar shi.

Wata abokiyar mamacin da ke a garin Jega da ta bukaci a sakaya sunan ta, ta ce tun da dadewa ya ke ce mata zai kashe kan sa idan matsanancin talaucin da ya ke fama da shi bai rage ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar da afkuwar lamarin, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai.