Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a JAMB, a karkashin jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, ta sake zama domin tattaunawa a kan mafi karancin makin jarabawar wannan shekara.
A taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandare na 19, an amince da maki 160 a matsayin mafi karanci domin samun gurbin karatu a jami’o’in gwamnati na shekara ta 2019.
Taron, wanda ya gudana a dakin taro na Bola Babalakin a jihar Osun, an kuma amince da maki 140 a matsayin maki mafi karanci domin shiga jami’o’i masu zaman kan su.
Haka kuma, an amince da maki 120 domin shiga Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na gwamnati, sa’annan maki 110 domin shiga Kwalejojin Kimiyya da Fasaha masu zaman kan su.
You must log in to post a comment.