Home Labaru Sakamako: Amurka Ta Karrama Limamin Da Ya Ceci Kiristoci A Jos

Sakamako: Amurka Ta Karrama Limamin Da Ya Ceci Kiristoci A Jos

246
0

Gwamnatin Amurka ta karrama Limamin da ya ceci Kiristoci 262 daga wasu mahara ya boye su a masallacin da ke jikin gidan sa.

Dan shekaru 83, Abubakar Abdullahi ya karbi lambar yabo ta ‘Yancin Addini ta duniya tare da wasu mutane hudun daga kasashen Cyprus da Sudan da Brazil da kuma Iraki.

Abubakar Abdullahi

Idan dai ba a manta ba, Limamin ya ceci Kiristocin ne a Barkin Ladi na Jihar Filato yayin da su ke neman mafita.

Limamin ya shaida wa manema labarai cewa, ya yi taimakon ne saboda fiye da shekaru 40 da su ka gabata Kiristocin yankin su ka kyale Musulmai su ka gina masallaci.

A wajen taron karramawar a karkashin jagorancin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Michael Pompeo, an ce Liman Abdullahi ya sa tasa rayuwar a hadari don ya ceto mabiya wani addini daban da ba na shi ba.

Kwanan baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da limamin aka kuma karrama shi da lambar yabo ta kasa. oun/��I��G