Home Labaru Bolaji Nagode Ya Zama Shugaban Cibiyar Horar Da Harkar Wutar Lantarki

Bolaji Nagode Ya Zama Shugaban Cibiyar Horar Da Harkar Wutar Lantarki

212
0
Ahmed Bolaji
Ahmed Bolaji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mista Ahmed Bolaji Nagode a matsayin shugaban cibiyar horar da harkar wutar lantarki ta kasa NAPTIN.

A cikin wata wasika da ke tabbatar da nadin daga ma’aikatar wutar lantarki, nadin zai shafe tsawon wa’adin shekaru hudu ne, kuma ya fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yuni na shekarra ta 2019.

An dai haifi Bolaji Nagode ne a ranar 10 ga watan Augusta na shekara ta 1962, sannan ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, da jami’ar Ilorin da kuma jami’ar Lagos.

Bolaji ya kasance mataimakin shugaban kamfanin wutar lantarki na Nijeriya, kafin daga bisani aka nada shi mataimakin darakta a cibiyar NAPTINS a cikin watan Fabrairun na shekara ta 2013.

Ahmed Bolaji, ya kasance rike da mukamin mukaddashin shugaban cibiyar horar da harkar wutar lantarki ta kasa daga shekara ta 2016 kafin wannan sabon nadi.