
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Nijeriya ta na maraba da karin kudirori da sa hannun jari a kan fasahar lataroni, yayin da ya yaba da shirin kafa Cibiyar Raya Afirka ta Microsoft da za ta ci dala miliyan 200.
Da ya ke karbar bakuncin shugaban Sashen Kasuwanci na kamfanin Microsoft Brad Smith tare da rakiyar Ministan Sadarwa da Tattalin arziki da Fasahar zamani Farfesa Isa Ali Pantami, Buhari ya ce an sanar da si cewa Cibiyar Raya Afirka a Nijeriya za ta zama cibiyar injiniya ta farko ta Microsoft da za a kafa a kan kudi dala miliyan 200.
Ya ce an kuma sanar da shi cewa shirin fasahar Microsoft, zai horar da ‘yan kasa miliyan biyar da kuma samar da ayyukan yi dubu 27 a cikin shekaru uku masu zuwa.
Shugaba Buhari ya shaida wa tawagar Microsoft cewa, a matsayin ta na kasa mafi karfin tattalin arzik,i kuma mafi yawan al’umma a Afurka, an sa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a tsarin fasahar zamani na kasa da kasa tare da neman hadin gwiwa don amfani da abubuwan da za a iya samu.
You must log in to post a comment.