Home Home Ciyarwa: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Al’ummar Musulmi Masu Hannu Da Shuni

Ciyarwa: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Al’ummar Musulmi Masu Hannu Da Shuni

66
0
Ciyarwa: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Al’ummar Musulmi Masu Hannu Da Shuni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya murnar ganin watan Ramadan.

A cikin sakon taya murnar, shugaba Buhari ya yi kira ga Musulmai su yi amfani da wannan dama wajen ciyar talakawa da marasa galihu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda shugaba Buhari ya ce lokacin azumi dama ce dake nuna wa masu hannu da shuni irin yunwar da talaka ke fama da ita kullum.

Shugaba Buhari, ya shawarci Musulmai su daina asarar abinci da almubazzaranci, yayin da wasu ke fama da yunwa da kunci, sannan ya yi kira ga Musulmai su rika tunawa da makwaftan su talakawa da marasa karfi.