Home Home Sadarwa: Majalisa Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Karin Kudin Da Aka...

Sadarwa: Majalisa Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Karin Kudin Da Aka Bullo Da Shi

43
0
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya kafa kwamitin wucin-gadi na mutane bakwai a karkashin jagorancin mataimakin mai tsawatarwa Aliyu Sabi Abdullahi, wanda zai binciki karin kudin fito da masu kamfanonin hada-hadar shirye-shiryen talabijin da ke aiki a Nijeriya su ka bullo da shi.

Matakin ya biyo bayan wani kuduri mai dauke da korafi da sanata Abba Moro ya gabatar a zauren majalisar, inda ya ce akwai koken da ‘yan Nijeriya ke yi game da yawan karin kudin fito da kamfanonin ke yi babu kakkautawa.

Abba Moro ya koka da cewa, ‘yan kasa su na biyan kudi da yawa, amma ba su morar kudin saboda kalubalen da Nijeriya ke fama da shi na wutar lantarki.

Mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce kwamitin zai yi aiki bil-hakki da gaskiya.