Home Home Korafi: Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta Ce Cin Zarafin Mata Da Yara...

Korafi: Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta Ce Cin Zarafin Mata Da Yara Ya Na Karuwa

48
0
Hukumar kare hakkin bil’ada ta Nijeriya reshen jihar Kano, ta nuna damuwa a kan yadda adadin magidantan da ke cin zarafin mata da kananan yara ke karuwa a baya-bayan nan.

Hukumar kare hakkin bil’ada ta Nijeriya reshen jihar Kano, ta nuna damuwa a kan yadda adadin magidantan da ke cin zarafin mata da kananan yara ke karuwa a baya-bayan nan.

Ofishin hukumar, ya ce daga watan Janairu zuwa karshen watan Maris da ya gabata, ya karbi korafe-korafen cin zarfin mata a cikin gidaje da kananan yara da yawan su ya kai kimanin dari uku.

A cikin wani rahoton watanni ukun farkon shekara da hukumar ta wallafa, ta ce adadin ya kunshi matsalolin da su ka shafi zamantakewa tsakanin ma’aurata, da batutuwan da su ka shafi yara na aikatau da fyade da kuma tallace-tallace.

Jami’in Hukumar na shiyyar Kano Malam Shehu Abdullahi, ya ce abin damuwa ne yadda zamantakewar ma’aurata ke kara dagulewa, lamarin da ke kara jefa makomar yara cikin yanayi na rashin tabbas.