Home Labarai Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Za a Yi Amfani Da Jiragen Super...

Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Za a Yi Amfani Da Jiragen Super Tucano Lokacin Da Ya Dace

330
0

Fadar shugaban kasa ta kare matakin jan kafar tura jirgin yaki
samfurin Super Tucano, domin yakar ‘yan bindiga a yankin
arewa maso gabashin Nijeriya.

Ta ce kafin gwamnati ta sayi jiragen yakin daga Amirka, akwai
yarjejeniyar da za a cimmawa gabannin cinikin game da batun
take hakkin dan adam.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da
haka, inda ya ce ana ba sojoji horo ne.

Ya ce shugaban kasa ya san abin da ya ke yi, fatan su kawai shi
ne, da zarar ya kammala wa’adin mulkin sa kotun hukunta
manyan laifuffuka ta duniya bata ta gayyace shi saboda take
hakkin dan adam ba.

Garba Shehu, ya ce a bayyane ta ke karara cewa Amurka ta
saida wa Nijeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano, amma
ana bin tsarin da dokoki su ka tanada wajen tabbatar da hakan.

Leave a Reply