Home Labaru Sabuwar Kaka: Kano Pillars Za Ta Buga Wasannin Ta A Filin Wasa...

Sabuwar Kaka: Kano Pillars Za Ta Buga Wasannin Ta A Filin Wasa Na Sani Abacha

5
0
Hukumar kula da gasar ƙwallon ƙafar ƙwararru ta Nigeria (NPFL) ta amince wa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ci gaba da amfani da filin wasan ta na Sani Abacha da ke Kano a kakar wasa ta 2021 zuwa 22.

Pillars ta fara amfani da filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna ne a matsayin filin was an ta na gida tun bayan ɓullar annobar korona, abin da ya sa aka mayar da filin wasa na Sani Abachan wurin killace masu jinyar cutar.

NPFL ta ce duk da cewa hukumar League Management Company LMC mai jan ragamar gasar ba ta sanya ranar fara sabuwar kakar wasan ta 2021 zuwa 2022 ba, ta amince a yi amfani da Sani Abacha bayan zagayen duba shi da jami’anta suka yi kamar yadda Pillars ta sanar.

Ƙungiyar Akwa United ce dai ta lashe gasar da aka kammala ta 2020 zuwa 21.