Masu yi wa ƙasa hidima a Jihar Zamfara sun shiga halin fargaba sakamakon sace abokan su da wasu ‘yan bindiga suka yi a kan hanyar su ta zuwa sansanin horarwa na karamar hukumar Tsafe.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfaran ta tabbatar da sace masu hidimar biyu, sai dai wasu da suka shaida lamarin na cewa mutanen da aka sace sun zarta haka.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu, ya ce kwamashinan ‘yan sanda Ayuba Elkana ya ziyarci sansanin, inda ya tabbatar wa jami’an hukumar NYSC yunƙurin sa na kare rayukan ‘yan yiwa kasa hidiman.
A ranar Larabar da ta gabata ne wani ɓangare na sabbin masu yi wa ƙasa hidiman a faɗin Najeriya suka shiga sansanoni don karɓar horo biyo bayan kammala manyan makarantu.