Home Labaru Sabuwar Dokar Zabe: Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Yi Bita

Sabuwar Dokar Zabe: Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Yi Bita

14
0

Kwamitin mutum 7 da Majalisar Dattawa ta nada, ya shirya yin bitar sabuwar dokar zabe, musamman sashen da ya ce hukumar zabe za ta iya aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo, amma ‘yan adawa na cewa dama zamba aka shirya yi a sabuwar dokar Zaben.

Nada Kwamitin mutumin ya samo asalin ne akan takkadamar da ta kunno kai kan ba wa hukumar zabe damar aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo, bayan an kammala Zaben.

Wannan batu ya raba kan ‘yan majalisar dattawan, inda a karshe aka ce ba zai yiwu ba, amma hukumar zabe ta fito fili karara ta ce za ta iya amfani da yanar gizo wajen aikawa da sakamakon zaben.

A yanzu dai sashi na 52 karamin sashi na 3 na dokar ita ce abin dubawa a sabuwar dokar zaben ta shekara 2021 wacce za ta maye gurbin dokar zabe ta shekarar 2010.