Home Labaru Mulkin Najeriya: Ali Modu Sheriff Ya Ce Suna Bukatar APC Ta Shekara...

Mulkin Najeriya: Ali Modu Sheriff Ya Ce Suna Bukatar APC Ta Shekara 50

14
0

Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif ya ce ya zama wajibi jiga-jigan jam’iyyar APC su yi aiki tukuru muddin suna son ganin mafarkin su na shafe shekara 50 tana mulki a Najeriya ya zama gaskiya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a nan Abuja a ranar Lahadi.

Sanata Ali Modu, wanda daya ne daga cikin masu zawarcin Shugabancin jam’iyyar a matakin kasa ya ce dole sai sun yi aiki tukuru wajen ganin APC ta ci gaba da mulki bayan karewar wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Sanata Sheriff ya ce, a matsayin su na babbar jam’iyya, shekarar su shida kacal a kan karagar mulki, babban burin su shi ne APC ta shafe shekara 50 tana mulkin Najeriya.

Tuni dai tsofaffin Gwamnoni da wasu jiga-jigan jam’iyyar ta APC suka fara zawarcin shugabancin ta, duk da cewar jami’iyyar ba ta kammala yanke shawara kan shiyyar da za ta kai kujerar ba.