Home Labaru Sabon Sarki: Gwamnatin Kano Ta Nada Aminu Ado Bayero

Sabon Sarki: Gwamnatin Kano Ta Nada Aminu Ado Bayero

615
0
Sabon Sarki: Gwamnatin Kano Ta Nada Aminu Ado Bayero
Sabon Sarki: Gwamnatin Kano Ta Nada Aminu Ado Bayero

Gwamnatin jihar Kano ta nada Aminu Ado Bayero, a matsayin sabon Sarkin Kano bayan tsige tsohon Sarki Muhammadu Sunusi II.

Kafin nada shi sarkin Kano, da ga tsohon Sarki marigayi Ado Bayero, Aminu Ado, shi ne Sarkin Bichi, daya daga cikin sabbin Masarautu 4 da gwamnatin Kanon karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira a shekarar bara.

Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin Kano ta hannun sakataren ta Alhaji Usman Alhaji, ya ce matakin zabar Aminu Ado Bayero, a matsayin Sarki ya biyo bayan amincewar majalisar masu zabar Sarki a masarautar ta Kano ne.

Ya kara da cewa gwamnatin Kano ta tsige tsohon Sarki Muhammadu Sunusi, na 2 ne bayan tuhumar sa da laifin wulakanta al’adun al’umma da masarautar da ya jagoranta, harma da gwamnati.