Home Labaru Alkawari: Dalung Ya Ce Gwamnatin APC Ba Ta Kammala Abinda Ta...

Alkawari: Dalung Ya Ce Gwamnatin APC Ba Ta Kammala Abinda Ta Fada Ba

291
0
Alkawari: Dalung Ya Ce Gwamnatin APC Ba Ta Kammala Abinda Ta Fada Ba
Alkawari: Dalung Ya Ce Gwamnatin APC Ba Ta Kammala Abinda Ta Fada Ba

Tsohon ministan wasanni, Salomon Dalung, ya bayyana wasu al’amurra game da yadda gwamnatin APC ke tafiya.

Solomon Dalung, ya ce shi ko kadan bai ji haushin kin maidashi kujerar ministan wasanni ba a wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu.

Dalung, ya ce Jama’a ba za su fahimci dangatakar dake tsakanin sa da shugaba Buhari ba, domin an dau tsawon lokaci suna tare tun lokacin da shugaba Buhari ya fara gwagwarmayar siyasa.

Y ace har yau suna na tare da Buhari, dan ya yi gwagwarmaya domin a zabe shi ne ba don neman abin Duniya ba, sai dan kasa ta samu cigaba.

Game da alkawuran da  jam’iyyar APC ta yi wa al’umma kuwa Dalung, ya ce haryanzun ba a kai ga cika su ba.

Duk da Solomon Dalung, ya tabbatar da cewa akwai sauran aiki a gaban gwamnatin Buhari, ya nunar da cewa ya na sa ran akwai lokacin da za a cika wadannan alkawurra baki daya.