Home Labaru Gwamnan Anambra Obiano Ya Kai Karar Malami Wajen Buhari

Gwamnan Anambra Obiano Ya Kai Karar Malami Wajen Buhari

17
0
Malami, Abiano da Shugaba Buhari

Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano, ya kai karar Ministan Shari’a Abubakar Malami ga fadar shugaban kasa, sakamakon furucin da ya yi cewa mai yiwuwa a sa dokar ta-baci a jihar sa.

Jihar Anambra dai ta kwashe tsawon watanni ta na fama da rigingimu masu nasaba da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wannan ya sa Abubakar Malami ya shaida wa manema labarai cewa, akwai yiwuwar a ayyana dokar ta-baci a jihar idan matsalar tsaro ta cigaba da ta’azzara.

Kalaman Ministan dai su na zuwa ne, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan a jihar a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Sai dai bayan ganawar sa da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja, gwamna Obiano ya shaida wa manema labarai cewa bai ji dadin kalaman Abubakar Malami ba, ya na mai cewa tuni ya san batun sa dokar ta-baci ba ya cikin tsarin shugaba Buhari, domin ya san Anambra na daya daga cikin jihohi masu zaman lafiya a Nijeriya.