Home Labaru Saba Ka’ida: Kotun Soji Ta Rage Wa Janar Olusegun Adeniyi Mukami

Saba Ka’ida: Kotun Soji Ta Rage Wa Janar Olusegun Adeniyi Mukami

159
0

Wata kotun soji a Najeriya ta samu tsohon kwamandan rundunar yaƙi da Boko Haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi, da laifin saɓa ƙa’idar amfani da shafukan sada zumunta.

An samu janar din da laifin ne yayin da yake bakin aiki sakamakon an gan shi a wani faifen bidiyo a watannin baya a shafukan intanet yana korafin cewa ba su da isassun makamai na yaki da Boko Haram.

Mai Magana da yawun rundunar sojan Najeriya ya tabbatar wa cewa kotun ta yanke hukuncin cewa a rage masa mukami.

Wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa hukuncin ya biyo bayan saɓa ƙa’idar dokar soji da janar din ya yi ne wadda ta haramta yaɗa bayanai game da ayyukan su a intanet.

Olusegun Adeniyi ya ɗauki bidiyon ne tare da sauran dakaru a wani fili jim kadan bayan ‘yan bindiga sun kashe gomman sojoji a Jihar Yobe a farkon wannan shekarar.