Home Labaru Ci Gaba: Biden Ya Ba Dan Najeriya Mukamin Mataimakin Ma’ajin Baitil Malin...

Ci Gaba: Biden Ya Ba Dan Najeriya Mukamin Mataimakin Ma’ajin Baitil Malin Amurka

101
0

Wani lauya haifaffen Najeriya kuma tsohon babban mai ba shugaban Amurka Barack Obama shawara kan tattalin arzikin duniya, Adewale Adeyemo, zai zama sabon mataimakin ma’ajin baitil malin Amurka.

Adeyemo, zai yi aiki ne tare da Janet Yellen, bayan da zaɓaɓɓen Shugaban kasar Amurkan Joe Biden ya zaɓe su a matsayin ma’aji da mataimakin baitil malin ƙasar.

Muƙamin Adeyemo, na ɗaya daga cikin muƙaman da ake sa ran Biden, zai sanar da su nan ba da jimawa ba.

An haifi Adewale Adeyemo, da aka fi sani da Wally, ne a shekarar 1981 a Najeriya, amma ya girma a California na kasar Amurka.