Home Labaru Neman Mafaka: Katsinawa Na Gudu Zuwa Kaduna Su Kwana Saboda Firgici

Neman Mafaka: Katsinawa Na Gudu Zuwa Kaduna Su Kwana Saboda Firgici

118
0

Rahotanni daga Jihar Katsina na cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mutum bakwai cikin kwana uku a yankin ƙaramar ƙukumar Sabuwa ta jihar.

Ɗan majalisar jihar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Sabuwa, Ibrahim Ɗanjuma Machika, ya shaida cewa an kashe mutanen ne tsakanin Tashar Bawa zuwa Ɗan Kolo da ke yankin.

Ya ce mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe ba ‘yan yankin ba ne, domin an kashe su ne yayin da suke tafiya a cikin irin motar Ɗangote, sauran biyar kuma asalin ‘yan yankin ne, kuma tuni aka yi musu jana’iza.

Honourable Ɗanjuma ya shaida cewa babban abin da ya tayar masa da hankali kan wannan harin, shi ne wata mata da goyonta da aka kashe.

Ya bayyana cewa rashin tsaron da ke addabar yankin ya kai ga cewa mutanen da ke garin Tashar Bawa ba su iya kwana cikin garin yain da wasu ke gudu zuwa Kaduna.

An tuntuɓi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah, domin jin ƙarin bayani kan lamarin, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan adadin da aka kashe inda ya yi alƙawarin bada bayani a nan gaba.