Home Labaru Saba Ka’ida: Gwamna Aminu Masari Zai Kafa Dokar Haramta Kiwo

Saba Ka’ida: Gwamna Aminu Masari Zai Kafa Dokar Haramta Kiwo

17
0

Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin jihar na shirin kafa dokar haramta yawon kiwo a jihar.

Masari ya jaddada sukarsa ga yawon kiwo da cewa ya saba wa Musulunci, yana mai cewa ya kamata makiyaya su tsaya a guri guda su kiwata dabbobinsu.

Gwamna Masari ya kara da cewa Gwamnatin jihar Tana so ta kafa dokar haramta yawon kiwo, amma kafin mu yi hakan za mu samar da wuraren da dabbobin za su yi kiwo.

Ya kara da cewa ya kamata makiyaya su tsaya a wuri guda domin yawon kiwo ya saba wa Musulunci.

Ya kuma soki lamirin yadda mutum zai tara dabbobin da ba zai iya ciyarwa ba, su rika shiga gonakin mutane, wanda hakan ba dai dai bane,

Masari yace Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira bililyan N6.2, mu kuma a matsayin gwamnatin jiha za mu ba da Naira biliyan 6.2. Manufar ita ce ganin Fulani sun zauna a wuri daya sun daina yawon kiwo.”

Tuni dai gwamnatocin jihohin da ke yankin Kudancin Najeriya suka kafa dokar haramta yawon kiwo a fadin yankin.