Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane A Kwalejin Ilimi Ta...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane A Kwalejin Ilimi Ta Katsina

20
0

’Yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma a Jihar Katsina inda suka yi awon gaba da ’ya’yan Mataimakin Shugaban Kwalejin su uku.

Masu garkuwar sun kutsa gidan Mataimakin Kwalejinn da ke harbar makarantar ne dauke da makamai, suka tisa keyar ’ya’yan nasa maza uku.

Rahotanni sun tabbatar da cewar a jiya Litinin da misalin karfe 11:30 na dare, wasu mutum hudu dauke da muggan makamai suka shiga Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma inda suka shiga gidan Mataimakin Shugaban Kwalejin, Dokta  Isma’il Ado Funtua, suka yi awon gaba da ’ya’yansa maza su uku.Lokacin da da suka isa gidan sun samu mai gadin ba ya nan, an dai makala wani kwado a jikin kofar ta cikin gidan, sai suka cire kwadon suka shiga cikin gidan.

Majiyarmu ta ce a hanya ne masu garkuwar suka saki mai gadin, suka wuce da matasan wadanda dukkanninsu dalibai ne a manyan makarantu.

Mun nemi samun karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, Gambo Isa, amma har muka kammala hada wannan rahoto bai amsa kiran wayar da muka yi masa ko rubutaccen sakon da muka tura masa ba.