Home Labaru Tsaro: Shugaban Kasa Ya Bayyana Cewa Zai Yi Sauye-Sauye

Tsaro: Shugaban Kasa Ya Bayyana Cewa Zai Yi Sauye-Sauye

19
0
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru
Buhari Ya Kalubalanci Manyan Hafsoshin Soji Su Kirkiro Sabbin Dabaru

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa manyan hafsoshni taro shirinsa na yin sauye-sauye a tsarin tsaron  kasa a lokacin da ya karbi bakuncin su inda suka gabatar masa da rahoton ayyukansu

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya ce Buhari ya shaida wa Manyan Hafsoshin Tsaron cewa zai ci gaba da yin canje-canje a wurin da bai gamsu ba a bangaren na tsaro.

Monguno, wanda ya yi wa manema labarai bayani bayan zaman a Fadar Shugaban Kasa, yace Buhari ya bayyana wa hafsoshin tsaron matsayinsa ne bayan sun gabatar masa da nasarorin da sojoji suka samu a yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Monguno ya ce Buhari ya nuna farin cikinsa kan nasarorin da rundunonin tsaro suke samu a halin yanzu a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya, ’yan fashi, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata miyagun laifuka a sassa daban-daban na kasar nan.

Mahalarta taron dai sun hada da Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi (mai ritaya) da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da manyan Hafsoshin Soji wadanda Babban Hafsan Soji, Janar Lucky Irabor ya jagoranta.