Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya karyata zargin da mataimakin sa Simon Achuba yayi cewa ya na farautar rayuwar sa, inda ya bukaci jama’a su yi watsi da zargin.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Onogwu Mohammed ya fitar, gwamnan ya ce zargin wani yunkuri ne na ganin makiya sun bata ma shi suna da kuma neman suna a wajen jama’a.
Gwamnan, ya bukaci mataimakin sa ya gabatar da hujjoji domin tabbatar da ikirarin sa na cewa ya na farautar rayuwar sa.
Idan dai za a iya tunawa, a baya mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa, Yahaya Bello ya ba ‘yan bindiga kwangilar kashe shi.