Home Labaru Romon Dimokradiyya: Buhari Ya Yi Alkawarin Kammala Ayyukan Da Aka Yi Watsi...

Romon Dimokradiyya: Buhari Ya Yi Alkawarin Kammala Ayyukan Da Aka Yi Watsi Da Su

337
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shaida wa babban basaraken Warri na jihar Delta cewa, ya na da alkaluman kuri’un da mutanen jihar Delta musamman kabilar Itsekiri suka kada masa a zaben shekara ta 2019.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da sarkin Warri mai martaba Ogiamen Ikenwoli ya ziyarce shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, domin neman alfarmar gwamnati ta gina tashoshin ruwa a yankin sa da wasu sassan kudu maso gabashin Nijeriya.

Olu of Warri

Mai martaba Ikenwoli, ya ce yin hakan zai taimaka wajen rage cunkuso a tashoshin ruwa da ke Legas, lamarin da ya ce ya na barazanar gurgunta tattalin arzikin jihar Legas.

Basaraken, ya kuma roki shugaba Buhari ya farfado da cibiyar sarrafa makamashin iskar gas da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gina, ya na mai cewa yin hakan zai samar da guraben aiyuka har dubu 250.