Rundunar sojin Nijeriya, ta shirya wa dakarun ta taro da
zummar fahimtar da su illoli da kuma darussan da ke tattare
da yakin basasa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Manjo Hashimu Sa’ad Abdullahi ya fitar, ta ce Kwalejin Koyar da Yaki ta Nijeriya ta shirya wa dakarun ta taro a kan bukatar waiwaye game da yakin basasar da aka yi a Nijeriya.
Sanarwar, ta ambato babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya na jaddada muhimmancin yin nazari a kan Yakin Basasar Nijeriya, saboda akwai manya- manyan darussan da za su taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta.
Ya ce yanayin rashin tsaro a yanzu ya na da sarkakiya da hatsari da kuma rashin tabbas, ya na mai cewa fahimtar tarihin kasa zai taimaka a gamsu da yadda aka kwashe shekara da shekaru wajen gina manyan ababen more rayuwa, wadanda ana iya rusawa a dan kankanen lokaci.
You must log in to post a comment.