Home Labaru Takarar Musulmi Da Musulmi Yaudara Ce — Baba-Ahmed

Takarar Musulmi Da Musulmi Yaudara Ce — Baba-Ahmed

1
0

Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa Hakeem
Baba-Ahmed, ya ce takarar Musulmi da Musulmi ba komai ba
ce illa tsagwaron yaudara.

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana haka ne, yayin da ya ke tsokaci game da mika takarar shugabancin majalisar dattawa da APC ta yi a hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, inda ya ce kamata ya yi a bar ’yan majalisa su zabi wanda su ke so ya jagorance su.

Ya ce ya kamata a bar yankin Arewa Maso Yamma ya samar da Shugaban Majalisar Dattawa, saboda kuri’un su ne su ka ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu nasarar lashe zabe.

Da ya ke tsokaci game da takarar Musulmi da Musulmi a Jihar Kaduna, Hakeem Baba-Ahmed ya ce kashi 95 cikin 100 na gidajen da gine-ginen da El-Rufa’i ya rushe na Musulmi ne. don haka yaudara ce kawai.