Home Labarai Rundunar Sojin Kasa Ta Sauya Wa Manyan Hafsoshi Wurin Aiki

Rundunar Sojin Kasa Ta Sauya Wa Manyan Hafsoshi Wurin Aiki

38
0

Shugaban rundunar sojin kasa Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya amince da nadi, da kuma sauya wa manyan sojojin kasa wuraren aiki a wani mataki na kara masu kaimin yaki da ta’addanci.

A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar soji
Birgediya janar Onyema Nwachukwu ya fitar a Abuja, ya ce
wadanda lamarin ya shafa sun hada da kwamandoji da sauran
manyan sojoji.

Nwachukwu, ya ce an tura Manjo janar Godwin Umelo zuwa
helkwatar tsaro daga cibiyar tsaro ta DSC a matsayin darakta
janar na binciken harkokin tsaro da ci-gaban yaki.

Janar Onyema ya kara da cewa, an sauya wa Manjo Janar V.
Ebhaleme matsayi zuwa daraktan sashen gudanarwa, yayin da
Manjo Janar GB Audu ya koma cibiyar bincike a matsayin
babban ma’aikaci.

Sauran sun hada da kwamandan Kwalejin yaki ta sojoji Manjo
Janar Solomon Udounwa, wanda ya koma shugaban shirin soji a
Helkwatar ayyukan musamman, yayin da aka maida Manjo
Janar MT Durowaiye zuwa hedkwatar soji da kuma daraktan
harkokin tsofaffin soji.