Home Labarai Kungiyar Kabilar Igbo Ta Ce Ba Ta Ji Dadin Kudirin Tinubu Na...

Kungiyar Kabilar Igbo Ta Ce Ba Ta Ji Dadin Kudirin Tinubu Na Tsayawa Takara Ba

102
0

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze, ta bayyana rashin jin daɗin ta game da matsayin da Bola Ahmad Tinubu ya ayyana na tsayawa takarar shugaban kasa.

Ohaneze Ta yi gargadi cewa, ya kamata Bola Tinubu ya yi taka
tsantsan domin yunƙurin shi ya na neman wuce makaɗi da rawa.

Wannan dai ya na zuwa ne, yayin da gwamnan jihar Ebonyi
Dave Omahi ya gana da Shugaba, inda shi ma ya bayyana
kudirin shi na tsayawa takarar shugaban kasa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Ohanaze ta ce
kuskure ne da ganganci Bola Tinubu ya bayyana aniyar sa ga
Shugaba Buhari ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekara ta
2023.