Home Labaru Dara Ta Ci Gida: ‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’in KASTELEA A Jihar...

Dara Ta Ci Gida: ‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’in KASTELEA A Jihar Kaduna

2668
0

Wasu gungun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kaduna KASTELEA, mai suna PMA II Hamza a kan hanyar Birnin Gwari bayan sun kashe mutane biyu daga ciki har da jariri.

Rahotanni sun ce ‘ yan bindigan sun kama Hamza ne a daidai lokacin da su ka tare wasu motocin haya guda 2 su ka bude masu wuta, lamarin da ya sa su ka kashe wani jariri da ke hannun mahaifiyar sa da wani mutum guda baya ga jikkata wasu mutane biyu.

Wata majiya ta ce jami’in na KASTELIA ya na kan hanyar sa ne ta komawa gidan sa da ke Birnin Gwari a ranar Juma’ar da ta gabata, kuma tun bayan faruwa lamarin har yau ba a samu labarin inda ya shiga ba. Bayan manema labarai sun tuntube shi domin jin ta bakin shi a kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya ce ba ya da masaniya game da lamarin sakamakon baya gari, kuma a ranar litinin ya dawo bakin aiki, sai dai ya yi alkawarin gudanar da bincike, amma har lokacin tattara wannan rahoto bai bada wani bayani ba.