Home Labaru Adamawa: An Cafke Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Babban Sakatare

Adamawa: An Cafke Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Babban Sakatare

276
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta jihar Adamawa, ta sami nasarar cafke mutane uku da ake zargi da hannunsu wajen aikata garkuwa da babban sakatare na ma’aikatar albarkatun kasa Emmanuel Piridimso.

Emmanuel,  ya afka tarkon masu garkuwa da mutane makonnin biyu da suka gabata, inda suka nemi kudin fansa naira miliyan 25.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Yahaya, ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto, yayin ganawa da manema labarai ta wayar tarho.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Yahaya,

Ya ce hukumar ‘yan sandan ta sami nasarar kwace ababen uku a unguwar Jimeta dake Arewacin birnin Yola da kuma kauyen Maijaro a karamar hukumar Song.

Ya ce cikin wadanda aka kama su na hannun ‘yan sandan domin ci gaba da gudanar  da bincike.