Home Labaru Rufe Iyakokin Kasa: An Kama Wasu Masu Laifi Da Ake Nema Ruwa...

Rufe Iyakokin Kasa: An Kama Wasu Masu Laifi Da Ake Nema Ruwa A Jallo

1392
0

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta ce an kama wasu masu laifi da ake nema ruwa a jallo bayan rufe wasu daga cikin kan iyakokin kasa.

Muhammadu Babandede Kwantrolan hukumar na kasa

Kwantrolan hukumar na kasa Muhammadu Babandede, ya tabbatar da haka a wajen rufe taron hukumomin hukumar wanda ya gudana a Legas.

Ya ce sabon tsarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wajen dakile dukkanin wasu muggan ayyuka da ake aikatawa da kuma shige da fice ba bisa ka’ida.

Babandede ya ce ba wai gwamnatin tarayya ta rufe kan iyakokin ne saboda tsangwamar masu gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba, ta yi hakan ne domin tabbatar da cewa ana bin doka da oda.